Zaki ya kashe mai share gidansa a Habasha

wani zaki a kejinsa
Image caption Daraktan wajen ajiye namun dajin Dr Musie Kiflom , yace rana ce mafi muni a tarihin wajen

Wani zaki ya kashe wani mai share inda aka ajiye shi, a wani gidan ajiye namun daji, a birnin Addis Ababa na Habasha.

Kisan Abera Sisay mai shekaru 52 a duniya, da sanyin safiya ya sa an rufe gidan ajiye namun dajin.

Abera wanda ya yi shekara guda yana aikin baiwa dabbobi abinci da share wajen ajiye su, ya manta bai rufe kofar kejin da zakin ke ci ba.

Sauran ma'aikatan gurin sun harbi sama sau biyu da bindiga, domin razana zakin amma a banza, kuma nan take mutumin ya mutu bayan zakin ya cije shi a wuya.