Tattaunawar kawo zaman lafiya a Mali

Ibrahim Boubacar Keita, Shugaban kasar Mali
Image caption Ibrahim Boubacar Keita, Shugaban kasar Mali

Kungiyoyin 'yan tawayen Arewacin Mali suna wasu shawarwari a Bamako, babban birnin kasar, da nufin cimma wata matsaya ta bai daya, kafin ganawar da aka shirya za su yi da sabon shugaban kasar, Ibrahim Boubakar Keita.

A karkashin 'yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a cikin watan Yunin da ya gabata, wajibi ne sabuwar gwamnatin Malin ta fara tattaunawar zaman lafiya da kungiyoyin 'yan tawayen, nan da ranar 2 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Taron, wanda ake yi a asirce a wani hotel na birnin Bamako, yana cike da tarihi saboda dukan kungiyoyin 'yan tawayen sun aika wakilai.

Sun hada da kungiyar 'yan tawaye Abzinawa ta MNLA, da ta 'yan tawayen Larabawa ta MAA, da kuma sauran kungiyoyin irinsu Gandakoy da Ganda-Izo, wadanda ke wakiltar manoma.

Sai dai kungiyoyin masu kaifin kishin Islama irin su MUJAO da Ansarudine ba sa halartar shawarwarin.