Jonathan da Gwamnoni za su kara tattaunawa

Image caption Batun ko Shugaba Jonathan zai yi takara ya janyo rarrabuwar kawuna a PDP

Bangarorin biyu da suke hamayya da juna a jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya sun amince su mayar da wukar, don samun zaman lafiya kafin su koma tattaunawa a ranar 7 ga watan Okotoba.

A daren ranar Lahadi ne Shugaban kasar Goodluck Jonathan ya jagoranci zaman inda bangaren 'sabuwar' PDP wanda gwamononi bakwai suka balle ya amince a cigaba da tattaunawa don samun maslaha.

Gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu wanda ya karanto jawabin bayan taron, ya ce har yanzu akwai sauran abubuwan da basu sasanta a kai ba, amma dai sun cimma yarjejeniyar koma wa teburin sulhu a wata mai zuwa.

Daga cikin bukatun bangaren da ya balle, hadda batun Shugaba Jonathan ya janye batun takarar shugabancin kasar a shekara ta 2015.

Taron na daren ranar Lahadi ya samu halarcin mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo, Cif Tony Anenih da gwamnonin jihohin Rivers,Niger,Jigawa,Kwara,Adamawa,Katsina,Gombe,Cross River da kuma Kogi

Karin bayani