An dakatar da sojojin Rwanda su 20 daga aiki

Sojin Uganda
Image caption An zargi sojojin da aka dakatar da aikata rashawa

Rundunar sojin kasa ta Uganda ta dakatar da jami'anta su ashirin, bayan an zarge su da aikata rashawa a lokacin da suke aiki tare da dakarun Tarayyar Afirka a Somalia.

Ana zargin jami'an sojin ne da saida kayan abinci da kuma man fetur da aka tanada domin sojojin. Cikin wadanda ake bincika akwai wani babban jami'in sojin Ugandan Brigadiya Michael Ondoga.

Uganda dai ita ce kasar data fi kowacce bada gudummuwar sojoji ga rundunar Tarayyar Afirka a Somalia, inda take da kusan sojoji dubu shida daga cikin jimillar sojoji dubu goma sha takwas da suke Somalian domin yakar 'yan Kungiyar nan ta Al Shabab masu kaifin kishin Islama

Karin bayani