'Bukatar kuduri mai tsauri kan Syria'

Image caption Wasu daga cikin wadanda aka kashe a Syria

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce Faransa da Birtaniya da Amurka za su bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da kuduri mai karfi a kan lalata makaman Syria masu guba.

A wata yarjejeniya wacce Rasha da Amurka suka jagoranta, Syria ta amince za ta bayyana adadin yawan makamanta masu guba cikin mako guda, sannan a lalata su daga nan zuwa tsakiyar shekara ta 2014.

Idan har taki bada hadin kai, za a cimma matsaya wajen amfani da karfin soji a matsayin zabi na karshe.

Mr Hollande da ministan harkokin wajensa Laurent Fabius, sun tattauna a kan batun Syria tare da Sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague da kuma na Amurka John Kerry a Paris a ranar Litinin.

A kwannan nan Syria ta amince ta shiga cikin sawun kasashen da suka amince da yarjejeniyar takaita makamai masu guba, kuma majalisar dinkin duniya ta ce kasar Syriar za ta sa hannu a kai a 14 ga watan Okotoba.

Karin bayani