An bindige mutane 12 a Amurka

Image caption 'Yan sanda sun killace wurin.

A Amurka, babbar jami'ar 'yan sanda ta birnin Washington, Cathy Lanier, ta ce an kashe mutane goma sha biyu sakamakon harbi da wasu 'yan bindiga suka yi a wani ginin sojan ruwan kasar.

An kashe daya daga cikin 'yan bindigogin biyu da ake zargin sun kai harin.

Ba a dai san ko da wacce manufa suka aikata kisan ba.

Ta ce akwai 'yan sandan da suka samu 'yan raunuka, yayin da suka kai dauki a wurin da lamarin ya auku.

An rufe majalisar dattawan Amirkan da ke kusa da wurin har sai an gano dan bindiga dayan da yayi saura.

Tuni dai shugaba Obama ya bayyana jimami dangane da lamarin.

Karin bayani