2020: Australia za ta nemi diyya

Firai ministan Australia, Tony Abbott
Image caption Kasashen Australia da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Amurka ne suka nemi bakuncin gasar, amma ba a zabe su ba

Shugaban hukumar kwallon kafa na Australiya, Frank Lowy yace watakila kasar ta nemi diyya, idan an sauya lokacin gasar cin kofin duniya zuwa hunturu.

Austaraliya ba ta samu nasarar daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na 2022 ba, duk da cewa ta kashe kimani fam miliyon 25.

Qatar ce ta samu nasarar daukar bakuncin gasar daga cikin kasashe hudu da suka nemi bakuncin gasar, amma a yanzu hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na tunanin sauya lokacin gasar zuwa hunturu.

Yanayi zafi a Qatar na kaiwa ma'aunin Celsius 50 a watan Yuni da Yuli, abin da ya sa FIFA ke tunanin yin gasar a lokacin bazara a karo na farko a tarihin gasar.