Janjo ya nemi afuwar masoya Swansea

Jonjo Shelvey
Image caption Jonjo Shelvey

Dan wasan Swansea, Janjo Shelvey ya nemi afuwar magoya bayan kulob din, bisa kuskuren da ya yi har sau biyu a wasan da suka yi da Liverpool.

Shelvey ya ce, ''Ina neman afuwar magoya baya bisa kuskuren da na yi, na taimakawa kungiyar Liverpool aka tashi wasa biyu da biyu''

Shelvey ya fara zurawa tsohuwar kungiyar tasa kwallo, daga baya ya yi kuskuren mayar da kwallon gida, abin da ya bai wa Daniel Sturridge damar farke kwallon.

Victor Moses ya jefa kwallo ta biyu a ragar Swansea, sakamakon kuskuren da Shelvey ya yi lokacin da yake son bai wa abokin wasansa kwallo, amma daga baya ya mikawa Michu kwallon da ya zurawa Liverpool.