'Yan kwadago sun yi jerin gwano kan albashi

'Yan kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya
Image caption 'Yan kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun yi jerin gwanon motoci zuwa majalisar dokokin Najeriya, domin neman majalisar wakilai ta jaddada matsayinta game da sauya tsarin albashin ma'aikata.

Shugabannin kungiyoyin na son idan majalisun biyu sun zo tattauna batun sauya tsarin albashin, majalisar wakilai kada ta sauya matsayinta.

Majalisar wakilai dai ta amince a bar tsarin biyan albashi kamar yadda yake.

Sai dai majalisar dattawa ta yanke shawarar sauya tsarin albashin ma'aikata, ta yadda gwamnatin tarayya za ta biya albashi daban da wanda jihohi za su biya.

Sauyi game da tsarin biyan albashin na dubu 18 mafi karanci, wani bangare ne na gyaran wasu sassan kundin tsarin mulki kasar.