Za a dinke baraka a jam'iyyar PDP - Obasanjo

Shugaba Goodluck Jonathan da Chip Olusegun Obasanjo
Image caption Bangaren PDP da ya balle, a baya ya gindaya sharuddan cimma sulhu da suka hada da kada Jonathan ya tsaya takara

Tsohon shugaban Najeriya, Chif Olusegun Obasanjo yace muddin aka kasa warware rikicin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, har ya kai ga rugujewarta, hakan zai zamo abin takaici.

Ya bayyana hakan a wata hira da BBC, inda ya kara da cewa muddin hakan ya faru, to zai zamo karo na farko a tarihin kasar tun bayan karbar 'yancin kai, ace jam'iyya mai mulki ta ruguje a lokacin da take jan ragamar kasar.

Amma Mr. Obasanjo ya bayyana kwarin gwiwar cewa, jam'iyyar za ta dinke barakar da take fuskanta.

Ya kuma ce shi da wasu shugabannin jam'iyyar sun tattauna kan yadda za a cimma sulhu, kuma sun mika shawarwarinsu ga shugaba Goodluck Jonathan.