An gano gawar wani dan bindiga a Austria

Sojojin kasar Austria
Image caption Sojojin kasar Austria

'Yansanda a Austria sun gano konanniyar gawar dan bindigar nan da ya hallaka mutane 4, kafin ya kulle kan shi a gida ya kuma banka wuta.

'Yansadan sun yi wannan ganowar ne bayan binciken da suka shafe sa'o'i suna yi a cikin gidan gonar mutumin dake garin Melk a arewacin Vienna.

Mai magana da yawun hukumar 'yansandan Roland Schersher ya ce lokacin da suke bincikawa, sun gano wani dakin sirri, da kofar ke boye a jikin bango.

Ya ce 'yansanda sun yi amfani da karfin tuwo ne kafin su iya bude dakin, amma kuma an cinna wuta a ciki, sai da suka yi kokari wajen kashe wutar.

Lamarin dai ya fara ne da tsakar daren Litinin, lokacin da mutumin ya bude wuta kan motar sintirin jami'an 'yansanda, inda ya hallaka dansanda guda, ya kuma sace wata motar 'yansandan, bayan ya sake hallaka wani jami'in dansanda ya kuma yi garkuwa da guda, wanda daga bisani shima aka tsinci gawarsa a gidan mutumin.