An gabatarwa masu sauraro shafin BBC Hausa

Image caption Sashin Hausa na BBC

Sashen Hausa na BBC ya gabatarwa masu sauraro shafinsa na Intanet wanda ake samu a wayoyin salula, don labarai da rahotanni.

An gabatar da shafin ne ga ma'abuta amfani da wayoyin salula dan tatsar labarai ta internet a kowanne lokaci.

Shafin na bbchausa.com wanda ake samu a intanet na samar da labarai cikin hotuna da bidiyo da kuma sauti inda za a iya sauraro shirye-shiryen da ake gabatarwa a rediyo a kullum.

Shugaban sashin Hausa na BBC, Mansur Liman ya bayyana a taron da aka yi a birnin Lagos na Najeriya cewar " a yanzu a saukake ake samun labarai a wayoyin salula".