'An kashe 'yan Boko Haram 150 a Borno'

Image caption 'Yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan Boko Haram 150 a wani samame da ta kai a sansanin 'yan kungiyar a makon da ya gabata a jihar Borno.

Rundunar ta ce an kashe mata sojoji 16 lokacin da aka yi musayar wuta a samamen inda suka kai a maboyar 'yan Boko Haram din.

Wasu rahotannin sun ce kawo yanzu wasu sojojin sun yi batar dabo.

Wani wakilin BBC ya ce dakarun sojin Najeriya na karin gishiri a labaran adadin 'yan Boko Haram din da suka kashe, inda suke gum a kan yawan jami'an da lamarin ya rusta dasu.

Jihar Borno dai na karkashin dokar ta baci tun a watan Mayu, a kokarin Shugaba Goodluck Jonathan na murkushe 'yan Boko Haram.

Karin bayani