'Yar Nijeriya ta ci sarauniyar kyau Musulma

Aisha Ajibola
Image caption Aisha Ajibola, Sarauniyar Kyau Musulma

Wata 'yar Najeriya mai suna Aisha Ajibola ta lashe gasar da aka kira ta fidda- mace musulma ta gari -- wadda aka shirya musamman domin mata musulmi na duniya.

An gudanar da gasar ce a birnin Jakarta na Indonesia a matsayin kishiya ga gasar zaben sarauniyar kyau ta duniya.

Mata 20 ne suka shiga gasar daga Indonesia, da Iran, da Nigeria, da Brunei da kuma Bangladesh. Alkalan gasar sun yi la'akari ne da imanin matan da basirarsu da kuma iya karatun al-Kura'ani .

Daga cikin kyautukan da zata samu har da kujerar Makkah.

Daga cikin kyautukan da aka ba ta har da kujerar Makkah.