PDP: Rikici ya kaure a majalisar wakilai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Majalisar Wakilai, Aminu Waziri Tambuwal

'Yan Majalisar wakilan Najeriya sun ba hammata iska a lokacin da bangaren jam'iyyar PDP da ya balle, ya nemi gabatar da jawabi a zauren majalisar.

Majalisar wakilan ta dawo daga hutun makwanni bakwai ne lokacin da 'yan 'sabuwar' PDP suka kai ziyara karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Kawo Baraje.

An samu hatsaniya ne bayan da 'yan majalisar dake biyayya ga Shugaba Goodluck Jonathan suka soma ihu, abinda ya janyo martani da 'yan daya bangaren.

An shafe kusan mintuna goma ana fada tsakanin 'yan majalisar.

Wakilin BBC daya halarci zaman Ibrahim Isa, ya ce yaga an keta rigar wani dan majalisa.

'Zaben 2015'

Daya daga cikin bukatun 'yan 'sabuwar' PDP shine kada Shugaba Jonathan ya tsaya takara a shekara ta 2015.

Kawo yanzu dai Shugaba Jonathan bai bayyana ko zai tsaya takara ba, ko ba zai tsaya ba.

Sai dai mukarrabansa da matarsa, Patience tuni suka soma yi masa kampe don ya tsaya zabe.

Jam'iyyar PDP ce ke kan mulki a Najeriya tun a shekarar 1999.

Mista Jonathan ya dare kan mulki ne a shekara ta 2010 lokacin da Shugaba Umaru Musa 'Yar'Adua ya rasu a kan mulki.

Ya kuma tsaya takara a inuwar jam'iyyar PDP a shekara ta 2011, inda ya lashe zaben da 'yan adawa suka ce an yi aringizon kuri'u.

Karin bayani