'Yan Afirka ta Kudu sun fara shan maganin bera

Image caption Matasa sun fi amfani da maganin bera domin su rika yin maye

A birnin Soweto na Afirka ta kudu, matasa-- maza da mata -- sun fara shan maganin bera domin ya rika sanya su maye.

Akasarin matasan, wadanda ba su wauce shekaru ashirin da haihuwa ba, suna taruwa ne a wani waje da ke kusa da digar jingi, inda suke shan sabuwar kwayar mai suna nyaope.

Wasu daga cikinsu suna tafiya ne kamar matattu don haka mutane ke jifansu.

Thuli tana daga cikin masu shaye-shayen, kuma cikin maye ta ce: ''Ina zuwa makaranta amma ban daina saboda ina shan kwaya. Na yi watsi da makaranta lokacin ina da shekaru 14''.

Ta kara da cewa ba ta da wani buri na amfanar da kanta a rayuwa.

Shekarun Thuli 16 amma ta kamu da matsananciyar lalurar shan kwayoyi kamar yadda da dama daga cikin 'yan kasar suke yi, lamarin da kan sa kullum ake samun karuwar masu shan miyagun kwayoyi.

Ita dai Nyaope wata kwaya ce mai kamar hoda --- wacce aka hada da hodar ibilis da maganin bera da kuma magungunan ciwon HIV.

Idan aka hada ta da tabar wiwi tana sa masu shanta a cikin tanbele.

Karin bayani