Syria: Assad ya kalubanci Amurka

Image caption Ana ganin Shugaba Assad na wani kamfe ne a kaikaice na neman samun karbuwa ga Amurkawa

Shugaban Syria Bashar Al assad ya kalubalanci kasar Amurka da ta bayar da kudin aikin lalata tsibin makaman gubar kasarsa, wanda ya ce zai kai dala biliyan daya.

A cikin wata hira da gidan tallabijin na Fox News, Shugaba Assad ya ce a shirye yake ya rabu da makaman gubar, amma yayi gargadin cewar aiki ne mai wuya kuma zai iya daukar shekara daya ana yi, musaman da yake ana cigaba da fada.

Ya kara nanata cewar sojojin gwamnati ba su da hannu da harin da aka kai da makaman guba a birnin Damascus watan jiya.

Ya ce ya kamata Shugaba Obama ya saurari abin da ya kira ra'ayoyin al'ummar Amurka masu hankali, lokacin da aka tambaye shi sakon da zai aika wa shugaban na Amurka.

Karin bayani