Artabu a garin Kerdasa na Masar

magoya bayan kungiyar yan uwa musulmi
Image caption magoya bayan kungiyar yan uwa musulmi

Hukumomin Masar sun ce akalla mutane talatin da takwas ne suka rasu yayin arangamar da ta auku tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi.

Yawancin wadanda suka jikata lamarin ya ritsa da su ne yayin da jami'an tsaro suka yi harbi a sama da kuma harba barkonon tsohuwa domin hana magoya bayan Morsi shiga dandalin Tahrir.

Ana bukukuwan ne wanda sojoji suka shirya a dandalin domin ciaka shekaru arba'in da yakin da Masar ta yi da Israila a shekarar 1973.

Zanga zangar ta yan uwa Musulmi ta bazu zuwa wasu garuruwa da birane a fadin kasar.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba