Ba ruwan Iran da nukiliya- Rouhani

shugaban Iran Hassan Rouhani
Image caption Rouhani ya ce ,''matsalar ba za ta kasance daga gare mu ba.''

A hirarsa ta farko da wata kafar yada labarai ta yammacin duniya tun da ya kama mulki.

Sabon shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana wata wasika da shugaba Obama ya aike masa da cewa mai amfani ce da za ta haifar da ci gaba.

Da ya ke tattaunawa da kafar yada labarai ta NBC News, Mr Rouhani ya yi magana kan irin kyawawan matakan da za su kai ga cimma muhimmiyar makoma a nan gaba.

Shugaban ya kuma ce yana da cikakken ikon yin yarjejeniya kan ayyukan nukiliya na Iran.

Shugaban ya kuma jaddada matsayin Iran na cewa ba ta da niyyar kera makaman kare-dangi.