Mali: Shugaba Keita na rantsuwar kama aiki

Image caption Shugaba Keita dai ya taba rike mukamin Firayin Ministan kasar ta mali

A yau Alhamis ne ake rantsar da sabon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita a karo na biyu, bayan da aka zabe shi a ranar 11 ga watan Agusta.

Ya dai zamo shugaban kasar ne bayan da ya kayar da babban abokin takararsa Soumaila Cisse a zagaye na biyu na zaben wanda aka yi bayan kawo karshen yakin basasar da ya raba kasar gida biyu tun a watan Maris na 2012.

Tuni dai da Shubannin kasashen duniya daban-daban suka fara isa a Bamako babban birnin kasar domin su shaidi bukin rantsarwar.

Tun a ranar 4 ga watan Satumba ne shugaban ya yi kwarya-kwaryar rantsuwar kama aikin, sai dai wannan ita ce ranstuwar kama aiki gadan-gadan.

Karin bayani