Jamus ta musanta taimaka wa Syria

angela merkel
Image caption An yi safarar sinadaran ne cikin shekaru biyar har zuwa 2006.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta musanta cewa sama da tan dari daya na wasu sinadaran guba da aka fitar daga kasarta zuwa Syria an yi amfani da su wajen yin makamai masu guba.

Shugabar ta sheda wa gidan talabijin din Jamus cewa sinadaran an yi amfani da su ne wajen yin abubuwa masu amfani.

sinadaran na hydrogen fluoride da ammonium hydrogen fluoride za a iya amfani da su wajen yin gubar sarin mai karya laka.

Merkel ta ce har yanzu jami'ai na binciken abubuwan da aka yi da sindaran.