Guguwa ta halaka mutane 97 a Mexico

Image caption Guguwar dai na tafiyar kilomita 120 ne a wata daya

Hukumomin kasar Mexico sun ce mutane 97 ne suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar mai hade da ruwa da ta afkwa kasar tun a farkon makonnan.

A kauyen La Pintada da ke kusa da gabar tekun Pacific, kasa ta rufta da kusan rabin garin.

An gano akalla gawawwakin mutane 15 kuma mazauna kauyen su kusan 70 sun bata , inji hukumomin.

Guguwar wadda aka kira da ' Tropical Storm Manuel' dai yanzu ta doshi arewaci, inda ta tilastawa daruruwa mutane barin gidajensu a jihar Sinaloa.

Karin bayani