Najeriya za ta halatta nadar hirar jama'a ta salula

Majalisar dattawan Najeriya ta kammala karatu na biyu, na wani kudirin dokar da zai baiwa jami'an tsaro ikon tatsar bayanai, daga wayoyi da sauran hanyoyin sadarwar al'umar kasar.

Wannan dokar, idan aka zartar da ita, za ta taimaka wajen kare jami'an tsaro ta fuskar shari'a, ta yadda za su tatsi bayanai ba tare da neman izini 'yan kasar ba.

A bangare guda kuma, 'yan majalisar sun ce kudirin dokar zai taimaka wajen haramta wa 'yan kasar, musamman miyagu tatsar wayar al'uma da nufin cutar da su ta yadda za a fitar da wani hukunci mai tsanani.

Saboda a cewarsu a halin da ake ciki babu wani hukunci na musamma da aka tanada don hukunta duk wanda aka kama da yi wa wani kutse cikin sirrinsa.