Marikana: 'Yan sanda sun sharara karya

Image caption Ma'aikata a Marikana

Hukumar bincike kan kashe-kashen da 'yan sanda suka yi wa ma'aikata 34 a mahakar ma'adinai a Afrika ta Kudu, ta zargi 'yan sanda da sharara karya a kan lamarin.

Hukumar binciken ta ce 'yan sanda sun boye bayanai, suka sharara karya wajen bada bayanai game da lamarin.

A cewarta, ta yi nazari kan dubban takardu kuma za ta kara wa'adin binciken zuwa karin kwanaki masu zuwa.

Wakilin BBC a kasar ya ce wannan ya kara fito da rashin kimar da 'yan sanda ke dashi a Afrika ta Kudu.

Shugaba Jacob Zuma ne ya kafa hukumar binciken bayan kisan da aka yi a watan Agustan bara.

An kashe 'yan sanda biyu lokacin lamarin da ya auku a mahakar ma'adinai ta Lonmin.

Karin bayani