'Babu mai iya cin galaba a fadan Syria'

Image caption Wannan dai magana ce da ba a saba jin ta fito daga baki wani babban jigo a gwamnati ba.

Wani babban minista a gwamnatin Syria ya ce fadan da ake yi tsakanin 'yan tawaye da sojojin gwamnati a kasar ya cije, saboda yanzu babu bangaren da ke da galaba kan abokin gabarsa.

A cikin wata hira da jaridar Guardian ta Birtaniya, mataimakin farai minista Qadri Jamil, ya ce gwamnatin kasar za ta kira da a tsagaita wuta karkashin sa idon jami'an sanya-ido na kasa da kasa.

Ga alamu dai Qadri Jamil wanda ake kira da mutumin Rasha a Damascus, yana kokarin yin shinfida ne ga aniyar kasar Rasha ta shirya wata tattaunawar kawo zaman lafiya ta gaske.

''Sai dai babu tantama 'yan adawa za su yi fatali da wadannan kalaman nasa; saboda suna cike da shakku kan duk wata maganar yin sauye-sauye daga gwamnati.'' Inji wani wakilin BBC a birnin Beirut.

Karin bayani