An yi yunkurin kashe Kakakin Jihar Taraba

Image caption An dawo da Gwamna Danbaba Suntai ne daga Amurka a cikin wani yanayi mai rauni.

Rahotannin daga Najeriya sun ce an yi yunkurin hallaka Kakakin Majalisar Dokokin jihar Taraba Hon. Haruna Tsokwa da yammacin ranar Laraba.

Wasu 'yan-bindiga ne suka bude wa Kakakin Majalisar Dokokin da 'yan tawagarsa wuta kan hanyar Jos zuwa Abuja; sai dai babu wanda ya rasa ransa.

Harin ya zo ne kwana daya bayan da Kakakin ya shaidawa wata kotu a Jalingo cewa wasikar da aka aika wa Majalisarsa da sunan Gwamna Danbaba Suntai ta bogi ce; a wata shara'a da Gwamnan ya shigar domin kalubalantar matakin da majalisar ta dauka na kin amincewa komawarsa bakin aiki.

Sai dai wani mataimaki na musamman ga Kakakin ya nisanta harin daga alaka da dambarwar siyasar jihar, inda ya ce 'yan fashi da makami ne suka kai farmakin, ko da yake dai ya ce basu nemi karbar komai daga tawagar ba.

Karin bayani