'Ana sace gangar mai 100,000 kullum a Najeriya'

Wajen ajiye mai a Najeriya
Image caption Fasa bututan mai da gina kananan matatun mai na bayan fage, ya zama ruwan dare a yankin Niger-Delta mai arzikin mai

Wani sabon rahoto da cibiyar Chatham House da ke London ta fitar, ya nuna cewa Najeriya na asarar akalla ganga dubu 100 ta danyen mai a kowacce rana.

Hakan na nufin kasar ta yi asarar kusan kashi biyar cikin dari na baki daya man da aka hako a watanni uku na farkon shekarar 2013.

Rahoton ya ce ana karkatar da man ne zuwa kasashen yammacin Afrika da Amurka da kasashen Turai da kuma kasashe da dama a nahiyar Asia.

Haka kuma rahoton ya ce kudaden da ake samu ta hanyar danyen man da aka karkatar, ana halalta su a cibiyoyin kudi na duniya tare da sayen kadarori a ciki da wajen Najeriya.

Matsalar satar mai na ci gaba a Najeriya, duk kuwa da ikirarin hukumomin kasar na daukar matakan magance ta.