SSS sun cafke 'yan Boko Haram a Abuja

Image caption Dakarun sojin Najeriya

Rundunar tsaro ta farin kaya, wato SSS a Najeriya ta ce wata rundunar hadin gwiwa ta jami'anta da sojoji ta kai samame wani gida inda 'yan kungiyar Boko Haram ke boye makamansu a unguwar Apo kusa da rukunin gidajen 'yan majalisar dokoki da ke babban birnin Tarayya, Abuja.

Ko da yake rundunar ba ta bayyana adadin wadanda suka rasa rayukansu a fito-na-fiton da ta ce an yi tsakanin jami'an da 'yan kungiyar ba, amma wadanda suka shaida faruwar al'amarin sun ce akalla mutane takwas ne suka mutu.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da ake samun karuwar munanan hare-hare da rahotanni ke cewa masu sanye da kayan sarki na soji ne kan kai su.

Lamarin dai kan haddasa hasarar rayukan mutane da sabu san hawa ba balle sauka ba.

Karin bayani