'Yan tawayen sun amince su tsagaita wuta

Garin Azaz na Syria
Image caption Masu sharhi sun ce akwai yiwuwar Amurka da wasu kasashen yamma, su baiwa kungiyar sojojin Syria da suka sauya sheka makamai

Kungiyoyin 'yan tawaye biyu, sojojin Syria da suka sauya sheka da kuma Jihar Musulunci a Iraq da Syria, sun amince su tsagaita wuta a garin Azaz, bayan shafe kwanaki suna fafatawa a tsakaninsu.

Kungiyar Jihar Musulunci wacce ke da alaka da kungiyar AlQaida, ta kwace garin Azaz dake arewacin kasar a ranar Laraba, daga hannun babbar kungiyar sojojin da suka sauya sheka na Syria dake samun goyon bayan kasashen yamma.

Fadan tsakanin kungiyoyin biyu ya janyo fargabar barkewar wani rikici, a tashin hankalin da Syria ke fama da shi.

Wakilin BBC yace bangarorin sun amince su yi musayar fursunoni, su kuma mayar da abubuwan da suka kwace.