Kamfanin Blackberry zai sallami ma'aikata

wayoyin Blackberry

Kamfanin wayar salula ta Blackberry na Canada ya ce zai rage kashi 40 cikin dari na ma'aikatansa.

Ma'aikata 4500 ne a kasashen duniya sallamar za ta shafa domin rage asara saboda rashin ciniki.

Darajar hannun jarin kamfanin ta fadi da kashi 90 cikin dari a shekaru biyar zuwa shida.

A farkon wannan shekarar kamfanin ya ci buri a kan sabon samfurin wayar da ya bullo da shi ta Blackberry 10.

Amma kuma kasuwar ta bayar da shi ba a yi cinikinta ba kamar yadda kamfanin ya sa rai.