Dokar hana fita a Kafanchan na tasiri

Jama'a a garin Kafanchan dake Kudancin jahar Kaduna a Arewacin Najeriya, sun fara bayyana halin kuncin da suka shiga bayan dokar hana shiga da fitar da aka saka a garin ta sa'o'i 24.

Wasu mazauna garin sun ce yanzu haka ko abin da za su ci ba su dashi, yayin da wasu kuma ke cewa dan abincin da suke dashi yana dab da karewa.

An dai dauki wannan matakin ne bayan wani fadan kabilanci da addini da ya barke a farkon makon nan wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mutane.

Tuni dai wasu rahotannin ke cewa yanzu haka masu ruwa da tsaki a yankin na can suna ganawa game da halin da ake ciki a garin na Kafanchan.