Pakistan ta saki Mullah Baradar

Mullah Baradar
Image caption Mullah Baradar

Gwamnatin Pakistan ta ce ta saki babban shugaban kungiyar Taliban ta Afghanistan da ta ke rike da shi, Mullah Abdul Ghani Baradar.

Mullah Baradar dai na daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ta taliban, kuma shi ne mataimakin shugabanta, Mullah Mohd Omar.

Jami'an Pakistan din sun ce suna fatan kungiyar zata taimaka wajan shirya taron sasantawar da ake san yi.

Jami'an Afghanistan sun ji haushe da kaman na shi, inda sukai zargin Pakistan da yin zagon kwasa ga kokarin su na samar da zaman lafiya a kasar.