An fara nazari kan bayanan makaman Syria

Image caption Sai dai masu sharhi na ganin ba za a iya kammala aikin cikin jaddawalin da aka tsara ba saboda lokacin yayi kadan kuma sharuddan sun yi tsauri.

Hukumar Haramta Amfani da Makaman Guba ta Duniya ta ce ta fara nazarin bayanan da kasar syria ta mika game da makaman gubar da ta mallaka.

Sai dai wani mai magana da yawun hukumar ta OPCW ya ce hukumar na jiran karin bayanai daga Damascus gabanin cikar wa'adin mika bayanan wanda ke karewa karshen ranar Assabar.

An dai yi imanin cewar Syria na da kimanin ton dubu daya na makaman gubar; kuma ta amince ta ba da cikakken jerin sunayen makaman gubar da take da kafin karshen ranar Assabar.

An tsara za a kammala lalata dukkanin rumbunan makaman gubar ne nan da karshen shekara mai zuwa a karkashin wata yarjejeniyar da Rasha ta jagoranci cimmawa.

Ana ci gaba da tattaunawa a Amurka kan kudurin kwamitin tsaro dangane da lalata makaman, sai dai har yanzu Rasha na adawa da a yi maganar hukuntawa kan Syria ko da kuwa ta ki ba da hadin kai.

Karin bayani