Guguwa ta soma ta'adi a kudancin China

Guguwa a China
Image caption Guguwa ta yi ta'adi a wasu bangarorin kudancin China

Wata Guguwa mai karfi da ba'a taba ganin irinta ba cikin shekaru talatin ta soma ta'adi a wasu bangarorin kudancin China.

Guguwar ta kada bishiyu da turakun wutar lantarki dama kwashe motoci akan tituna.

Rahotanni na hukuma sun ce akalla mutane uku sun mutu.

An rufe tashar jiragen ruwa ta Hongkong, daya daga cikin tashar jiragen ruwa mafi hada- hada a duniya.

An kuma wargaza tsarin lokacin tashi da saukar jiragen sama a daukacin yankin.

Haka kuma an dakatar da zirga zirgar jiragen kasa tsakanin garuruwan Guangzhou da Shenzhen da Zhuhai.

An kuma rufe makarantu a wasu birane goma sha hudu.

Karin bayani