Akalla mutane 16 sun halaka a Iraqi

Iraqi
Image caption Rahotanni sun ce an jikkata mutane fiye da talatin a harin.

Akalla mutane goma sha shida aka kashe a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tada bom a cikin 'yan Sunni a wajen wata jana'iza a babban birnin Kasar na Bagdad.

Rahotanni sun ce an jikkata mutane fiye da talatin a harin da aka kai a kewayen Dora.

Fashewar bom din na zuwa ne kwana guda bayan an kashe fiye da mutum saba'in a wani hari da aka kai kan masu makoki a garin Sadr inda 'yan Shi'a suka fi rinjaye.

Karin bayani