Jonathan na so a hada kai a yaki ta'addanci

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya ya bayyana damuwarsa game da harin Kenya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana ta'aziyyarsa ga Shugaban Kasa da kuma al'ummar Kasar kenya, bisa mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a rukunin shaguna na Nairobi.

Shugaban ya bayyana bakin cikinsa kuma ya ce dole ne Kasashen duniya su hadu wajen yaki da abin da ya kira ta'addanci.

Mr. Jonathan ya ce duk wani harin ta'addanci da aka kai a ko'ina a duniya, ya shafi duniya ne baki daya.

Shugaban ya kuma bayyana ta'addanci kamar wata cuta data bulla a wani bangare na duniya, daga baya kuma ta bazu zuwa sauran sassan duniya ciki har da nahiyar Afrika.

Karin bayani