Ana ci gaba da farautar maharan Kenya

Uhuru Kenyatta
Image caption Shugaban kasar Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi jawabi ga al'ummar kasar yayin da yan kungiyar al-Shabaab kimanin goma zuwa sha biyar suke ci gaba da yin garkuwa da jama'a a wata cibiyar kasuwanci a birnin Nairobi.

Uhuru Kenyatta yace kasarsa kansu a hade wajen yaki da mawuyacin hali.

Ya kara da cewa Kenya kasa ce mai kalbilu da al'adu da dama da kuma addinai daban daban wanda yace hakan shi ne karin karfin kasar.

Ya baiyana wadanda suka kai harin a matsayin masu mugun nufi wadanda yace akwai bukatar hukunta shugabanninsu.

Kungiyar Al Shabaab dai ta ce ita ke da alhakin kai harin a matsayin ramuwar gayya game da tura sojojin da Kenya ta yi domin su yaki masu tsatstsauran ra'ayi a Somalia.