Obama na son takaita mallakar bindiga

Barak da Michelle Obama
Image caption Obama da matarsa na makoki

Shugaba Obama ya sake baiyana bukatar yi wa dokokin mallakar bindiga a Amurka garambawul.

Obama ya yi kiran ne a taron addu'o'in jana'izar wadanda aka harbesu ranar Litinin din da ta wuce a sansanin sojin ruwa a Washington.

Mutane goma sha biyu ne dai suka mutu bayanda wani dan bindiga dadi ya bude wuta a sansanin.

Mr. Obama yace tashin hankalin da al'umomin Amurka ke fuskanta ya kamata ya haifar da daukar matakan kawo sauyi.

Da ya juya ga adawar da ya ke fuskanta daga majalisun dokokin Amurka game da tsananta sharadan mallakar bindiga, Mr. Obama yace siyasa ce ke kawo tarnaki amma al'umar kasar za su iya kawo sauyi.