Al- Bashir na son halartar taro a NewYork

Omar al-Bashir
Image caption Al_Bashir ya ce tuni ya kama otel din da zai zauna a NewYork

Shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, ya tabbatar da kudurinsa na halartar taron majalisar dinkin duniya a New York cikin wannan makon, duk da nemansa da kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya ke yi bisa zargin laifin kare-dangi a rikicin yankin Darfur.

Shugaba al-Bashir ya shaidawa manema labarai a Khartoum, cewa tuni ya kama otel din da zai zauna, inda ya kara da cewa ba ya fargabar Amurka za ta kama shi saboda ba ta amince da ikon kotun ba.

Kawo yanzu dai babu tabbas ko Amurka za ta ba shi biza, amma dai a baya mahukuntan kasar kan bar shugabannin da ba sa jituwa da su, su halarci taron na majalisar dinkin duniya.

Karin bayani