Burtaniya tayi maraba da sanarwar Iran

Tutocin Iran da Burtaniya
Image caption Shugaban Amurka da na Iran zasu gabatar da jawabi ga taron majalisar dinkin duniya.

Burtaniya tayi maraba da sanarwar da ta fito daga Iran ta baya bayan nan cewa tana bukatar inganta dangantakar ta da Kasashen yamma da kuma sassauci game da damuwar da ake nunawa kan shirinta na makamin nukiliya.

Yayinda yake magana bayan ganawarsa tare da takwaransa na Iran Mohammad Zaif, sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague ya ce lokaci yayi da Iran zata dauki matakai a aikace wadanda zasu tabbatar da kalamanta.

Wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya ya ce akwai tsammanin taron majalisar dinkin duniya zai haifar da wata sabuwar dangantakar Iran tare da Kasashen yamma.

A ranar Talata shugaban Amurka da na Iran zasu gabatar da jawabi ga taron majalisar dinkin duniyar.

Fadar White House ta ce bata fidda ran ganawar Shugabannin biyu ba.

Karin bayani