ILO: Ci da gumin yara ya ragu a duniya

Wasu yara masu aikin kwadago
Image caption Talauci na daga cikin abubuwan dake jefa yara cikin wannan hadari

Kungiyar kwadago ta duniya, ILO ta ce an samu gagarumar raguwar yaran da ake tursasa wa yin ayyukan karfi a duniya, da kusan miliyan 78 a shekaru hudu da suka wuce.

Ci gaban da aka samu a cewar kungiyar ya fi bayyana a tsakanin yara mata, inda aka samu raguwarsu da kashi 40 cikin dari.

Yayin da a bangaren yara maza kuma aka samu raguwar wadanda ake tursasa wa shiga aikin karfi da kashi 25 cikin dari.

A cewar rahoton na Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO, idan aka dubi sassa daban daban na duniya, har yanzu an fi samun yawaitar ci da gumin yara ko kuma sanya su aikin karfi a kasashen a Afirka kudu da hamadar sahara, inda fiye da kasha daya ciki biyar na illahirin yara dake yankin ke cikin aikin karfi na ci da guminsu.

A kasashen na Afirka irinsu Nijeriya dai, bayanai na nuni da cewa ayyukan ci da gumin yara da akan ga kananan yara na yi sun hada da aiki a gonaki, da daukar kaya ko dako, da da tallace-talace da kuma safarar su kansu yaran da manya kan yi da dai sauransu.

Sai dai ILO ta yi gargadin cewa har yanzu akwai yara miliyan 168 ko kashi 11 na baki daya yara dake cigaba da kasancewa a cikin wannan hali a duniya.