Shirin soma taron Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dinkin duniya
Image caption Za a tattauna batun rikicin Syria da dangantakar Iran da Kasashen duniya

A yau ake shirin soma babban taron majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na Amurka.

Rikicin Syria da dangartakar Iran tare da Kasashen yamma ne zasu mamaye tattaunawa a taron.

Shugaba Barack Obama na Amurka da sabon Shugaban Iran Hassan Rouhani zasu gabatar da jawabi ga taron.

Fadar white house tace ba a fidda ran wata ganawa ba, tsakanin shugabannin biyu, wacce ita ce irinta ta farko tun juyin juya halin Kasar.

A waje daya kuma sakataren Amurka John Kerry zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov domin kokarin warware bancance bancancen dake tsakaninsu kan yadda za a tabbatar da cewa Syria ta mika makamanta masu guba.