Kasashen Amurka da Iran zasu gana

Hassan Rouhani
Image caption Ganawa ta gaba da gaba tsakanin manyan jami'an Amurka da Iran karo na farko

Fadar White House ta tabbatar cewa sakataren hulda da kasashen waje na Amurka zai gana da sabon ministan hulda da kasashen waje na Iran a ranar Alhamis, abinda ke nuna yiwuwar kyautatuwar alaka tsakanin Iran da kasashen Yamma.

John Kerry da Muhammad Jawad Zarif za su gana ne a hedkwatar majalisar dinkin duniya da ke New York domin tattauna shirin nukiliya na Iran tare da ministocin kasashen wajen China, da Rasha, da Burtaniya, da Faransa, da kuma Jamus.

Wannan dai ita ce ganawa ta gaba da gaba tsakanin manyan jami'an Amurka da Iran karo na farko tun bayan juyin juya halin Islama na Iran a shekarar alif da dari tara da saba'in da tara.

Karin bayani