An soma makokin kwanaki 3 a Kenya

'Yan uwan wadanda suka mutu a harin Kenya
Image caption Sojin Kenya sun ce sun yi imanin an kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su

An soma makokin kwanaki 3 a Kenya domin girmama mutanen da suka rasa rayukansu a harin da 'yan bindiga suka kai kan wani rukunin shaguna a birnin Nairobi.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ne ya bayyana kawo karshen mamayar da 'yan kungiyar Al Shabab ta Somalia suka yi a cibiyar kasuwancin dake birnin Nairobi.

A cikin wani jawabi kai tsaye ta talabijin ne, Shugaban ya bayyana zaman makokin kwanaki uku na alhinin wadanda aka rasa.

Ya ce fararen hula guda sittin da daya ne suka hallaka, da jami'an tsaro guda shidda.

Amma kuma ana jin yawan matattun zai karu, saboda wani sashen cibiyar kasuwancin ya rufta, kuma ya danne mutane.