Kudin ajiyar Najeriya sun ragu

Image caption Shugaban babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi

Kudin da Najeriya ke ajiyewa a asusun ajiyar kudin kasashen waje ya ragu da kashi 2.34 cikin 100 wato ya koma kusan dala biliyan 46 a watan Satumba.

Hakan dai ita ce raguwa mafi yawa a cikin watanni bakwai da rabi da suka gabata.

Kazalika duk wani yunkuri da Babban Bankin Najeriya-CBN ya yi na ganin kudin kasar, Naira, ya samu tagomashi kan dala, ya sanya shi yana yin asarar biliyoyin dala.

A watan Agusta akwai dala biliyan 47 a asusun ajiyar kudin kasashen waje na Najeriya.

Alkaluman da aka wallafa a shafin intanet na Babban Bankin Najeriya a watan Janairun da ya gabata akwai dala biliyan 45.91 a asusun.

Hakan dai yana shafar tattalin arzikin kasar, lamarin da ya sa Ministar Kudi, Ngozi Iweala, ta sha bayyana cewa da kyar suke iya biyan albashi.

Karin bayani