Shakkar matata ce ta sa na daina shan taba —Obama

Image caption Obama ya ce shekararsa shida bai sha taba ba

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya yi watsi da dadaddiyar dabi'arsa ta shan sigari ne saboda yana shakkar matarsa Michelle Obama.

Mista Obama ya bayyana haka ne cikin raha yayin da yake yin hira da wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya.

Da alama Mista Obama bai san na'urar daukar magana tana nadar abin da yake fada ba a lokacin da yake maganar a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York ranar Litinin.

Mista Obama ya shaidawa wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam cewa ya kwashe kusan shekaru shida bai sha sigari ba.

Ya ce; ''Ban sha sigari ba saboda ina shakkar matata'', yana mai yin murmushi.

Mista Obama ya yi hirar ne da Maina Kiai, wani babban jami'i na Majalisar Dinkin Duniya, yana mai fatan cewa shi ma (Kiai) ya daina shan sigari.

Karin bayani