A shirye muke mu tattaunawa akan nukiliya-Rouhani

Hassan Rouhani
Image caption Iran tace bata barazana ga duniya

A wani jawabi ga taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya ce a shirye Iran take ta shiga tattaunawa game da shirinta na nukiliya.

Ya ce ya kamata a kyale Iran ta samar da makamashin nukiliya saboda dalilai na zaman lafiya, amma bata da niyyar samar da makaman nukiliya.

Mr Rouhani ya ce Iran ba barazana bace ga duniya ko kuma yankin, face kasa ce mai son zaman lafiya.

Shugaban na Iran ya kuma yi allawadai da takunkumin da kasashen duniya suka sanyawa Kasar sa, yana mai cewa suna zama wani tashin hankali ne akan jama'a.

Obama ya samu karfin gwiwa daga Rhouhani

Tunda farko a jawabin da ya yi ga taron majalisar dinkin duniyar, Shugaba Obama ya ce ya samu karfin daga sassaucin salon da Mr Rouhani yake dauke dashi.

Mr. Obama ya ce hakan zai haifar da yanayin yarjejeniya akan shirin nukiliyar Iran.

Amma fadar white house ta ce ba za'a gudanar da tattaunawa ba tsakanin shugabannin biyu kamar yadda aka yi tsammani.

Jami'an Amurka sun ce sun yi tayin a shirya ganawar amma hakan ya yiwa Iraniyawa wahala sosai

Karin bayani