Majalisa za ta binciki kisan matasa 7 a Abuja

Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar dattijan Najeriya ta bada umurnin a gudanar da bincike a kan kashe matasa bakwai da jami'an tsaro suka yi a unguwar Apo dake Abuja babban birnin kasar a ranar Juma'a.

Majalisar ta umurci kwamitocinta a kan tsaro da harkoki shari'a da kuma na 'yancin dan adam sun gudanar da bincike kan kisan.

Mutane akalla bakwai ne suka mutu a yayinda kusan 12 suka samu raunuka lokacin da sojoji da kuma jami'an tsaron farin kaya wato SSS suka yi samame a wani gidan da ba a kamalla shi ba a Apo dake Abuja.

A yayinda jami'an SSS ke zargin cewar sun farwa 'yan kungiyar Boko Haram ne, bincike ya nuna cewar 'yan ci-rani ne matasan da aka kashe wadanda ba suda wajen kwana a Abuja.

Karin bayani