Mutum guda ya rasu a zanga-zangar Sudan

zanga-zanga a Sudan
Image caption zanga-zanga a Sudan

Akalla mutum guda ne ya rasu a Sudan sanadiyyar zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur, daya daga cikin matakan matse bakin aljihun da gwamnatin kasar ta dauka.

Masu zanga-zanga a biranen Khartoum da Omdurman sun rika rera taken cewa "jama'a na neman kifar da gwamnati."

Ministan kudin kasar Ali Mahmoud yace matakan inganta tattalin arzikin da suka hada da karya darajar kudin Sudan, zasu karawa gwamnati kudin shiga zuwa dalar Amurka miliyan dari shida da tamanin.

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir dai ya kwashe shekaru ashirin da hudu bisa mulki, kuma kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya na tuhumarsa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur.