Za a kashe mutumin da ya yi jifa da yarinya

Jaririya 'yar China
Image caption Yarinyar ta mutu sanadiyyar raunin da ta samu, bayan Mr. Lei ya yi jifa da ita

Wata kotu a China ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da ya kashe wata yarinya 'yar shekaru biyu a Beijing.

Han Lei ya finciko yarinyar daga cikin keken tura jarirai, sannan ya yi jifa da ita lokacin da mahaifiyarta taki kaucewa motarsa a watan Yulin da ya gabata.

Ya yi kokarin gudu amma mutane suka kama shi, kuma yarinyar ta mutu 'yan kwanaki kadan da aukuwar lamarin.

Lamarin ya fusata al'ummar China musamman bayan Mr. Lei ya shaidawa kotu cewa ya na cikin maye ne, a lokacin kuma ya yi tsammanin kayan cefane ya watsar ba karamar yarinya ba.